Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin PDP Sun Ja Hankalin Hukumomin Tsaro Kan Barazanar Da Wike Ke Yi


Ministan babban birinin Tarayyar Najeroya, Abuja, Nyesom Ezenwo Wike
Ministan babban birinin Tarayyar Najeroya, Abuja, Nyesom Ezenwo Wike

Kungiyar gwamnonin ta bukaci shugabannin hukumomin tsaron Najeriya su dauki mataki akan barazanar da Wike ke yi, ta hura wutar rikici a jihohin kasancewar babu wanda ya fi karfin doka a kasar.

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun bukaci hukumomin tsaro su dauki mataki kan irin barazanar da Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, ke furtawa na haddasa rikicin siyasa a jihohin gwamnonin da suka yi yunkurin yin katsalandan a rikicin reshen PDP na jihar Ribas.

A Asabar din data gabata a birnin Fatakwal, an ruwaito Wike na cewar “na ji wasu gwamnoni na cewar wai zasu kwace jam’iyyar su baiwa wani. Ina tausayin irin wadannan gwamnoni saboda zan cinna wuta a nasu jihohin.”

Sanarwar da babban daraktan kungiyar gwamnonin PDP, Emmanuel Agbo ya fitar, tace babu wanda ya fi karfin doka sannan ta bukaci hukumomin tsaro su dauki mataki akan kalaman ministan.

Agbo ya kara da cewar, kungiyar gwamnonin ta bukaci shugabannin hukumomin tsaron Najeriya su dauki mataki akan barazanar da Wike ke yi, ta hura wutar rikici a jihohin kasancewar babu wanda ya fi karfin doka a kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG