Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Na Murnar Cika Shekaru 30 Da Fara Fitowar Super Eagles A Gasar Cin Kofin Duniya


Tawagar Super Eagles
Tawagar Super Eagles

Yau shekaru 30 da suka gabata, kwallayen da rashidi yekini da daniel amokachi da emmanuel amunike suka ci sun taimakawa tawagar super eagles yin bajinta a fitowarta ta farko.

Hukumar Kwallon Kafar duniya (FIFA) ta gudanar da bikin cika shekaru 30 da fara fitowar tawagar Najeriya a gasar cin kofin duniya a shekarar 1994, sa'ilin da tawagar Super Eagles ta razana takwararsu ta kasar bulgaria wacce ake hangowa nasara inda suka fara gasar da kafar dama.

Tawagar ta Super Eagles ta fara bayyana a gasar cin kofin duniya a shekarar 1994, inda ta kara da takwararta ta Bulgaria wacce ke cike da 'yan wasa masu basira.

Duk da cewar an baiwa Najeriya matsayin daya dara na takwarorinta na turai, duk da haka ana yi musu kallon raini har sai da ta lallasa kasar Bulgaria da ci 3 da nema.

Kwallon Rashidi Yekini, wanda ya fara ciwa Najeriya kwallonta ta farko a gasar cin kofin duniya da wadanda Daniel Amokachi da Emmanuel Amunike suka ci sun wadaci Super Eagles samun galaba akan Bulgaria, inda ta shelanta shigowarta fagen gasar ta duniya.

FIFA ta tuna fara shigowar Najeriya gasar a shafinta na x, fifa ta jinjinawa bajintar tawagar super eagles a gasar cin kofin duniya na shekarar 1994, ta hanyar wallafa hotunan kwallon da rashidi yekini da tawagar najeriyar suka ci, da taken, "shekaru 30 a yau, super eagles ta samu nasararta ta farko a gasar cin kofin duniya.

Bayan samun galaba akan Bulgaria, Najeriya ta yi rashin nasara a hannun Argentina kafin daga bisani ta doke kasar Greece domin samun gurbi a rukuni na gaba na gasar.

Rashin nasara da ci 2 da 1 a hannun Italiya a rukunin 'yan 16 Najeriya na nufin kawo karshen fafatawarta a gasar a matakin rukuni, saidai har yanzu bajintar data nuna a fitowarta ta farko na zuciyar magoya bayan wasan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG