Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Arewacin Najeriya Sun Bukaci Taimakon Amurka Wajen Shawo Kan Matsalar Tsaro


Na biyu daga hannun hagu, Hyacinth Alia (Binuwe), Abba Yusuf (Kano) da Umar Namadi (Jigawa) da Uba Sani (Kaduna) da Manir Dan Iya (Sokoto)
Na biyu daga hannun hagu, Hyacinth Alia (Binuwe), Abba Yusuf (Kano) da Umar Namadi (Jigawa) da Uba Sani (Kaduna) da Manir Dan Iya (Sokoto)

Gwamnonin, da suka hada da Dikko radda na Katsina, Abba Yussuf Kano, Umar Namadi na Jigawa, Dauda Lawal na Zamfara, Muhammad Nasir na Kebbi, Caleb Muftwang na Filato da Uba Sani na Kaduna, Umar Bago na Neja da Hyacinth Alia na jihar Benue sun yi wannan kira ne a birnin Washington DC.

WASHINGTON DC - Gwamnonin wasu jihohin arewa maso yamma da maso tsakiyar Najeriya sun bakci kasar Amurka ta taimaka musu wajen magance matsalar tsaro da ta addabi jihohinsu.

Mahalarta taron da Cibiyar Bunkasa Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya.
Mahalarta taron da Cibiyar Bunkasa Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya.

Daya bayan daya, gwamnaonin sun bayyana yadda batun rashin tsaro ke maida ci gaban jihohin baya tare da yin kira ga neman taimako daga Amurka ta fannoni da dama domin shawo kan matsalalolin

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce wajibi sun tinkarin wannan aiki tare domin kaucewa tufka da warwar.

“Ina jin yaki da batun rashin bai daya zai taimaka, saboda idan muka kora ‘yan bindiga zasu koma jihar Zamfara amma idan a can Zamfara ana daukar irin wannan mataki lokaci guda can ma za a turo su, to da haka zamu magance lamarin baki daya”, inji Radda.

A nasa jawabi, gwamnan jihar Zanfara Dauda Lawal wanda shima ya yi ra’ayi da gwamnan Katsina ya ce “idan muka yi kokarin magance wannan matsala zai taimaka wurin shawo kan manyan matsalolin dake addaban al’ummar mu, abin fari ciki shine zamu yi wannan aiki tare.

Duk da cewar jihohin arewa na fama da matsaloli musamman maso yamma, akwai jihohi kamar su Filato da Neja da Benue dake arewa maso tsakiya da gwamnoninsu suka halarci taron kuma suka bayyana irin matsaloli da suke fuskanta.

Gwamna Caleb Mftwang na Filato ya ce dole ne a tantance yanayin kowace jiha domin sanin yanda za a tinkari matsala ta kowace jiha kuma ya ce arewa ta tsakiya ta dade tana fama da matsalar tsaro kafin yankin yamma ta biyo sawu.

Ya ce “idan muka nemi shawo kan lamarin da salo iri guda ba zamu samu sakamakon da muke bukata ba, ya kamata a tantance sosai kuma a duba yadda kowace al’umma take, haka zai sa mu fahimci matsalolin su da kuma hanyar magance su.

Uba Sani na Kaduna ya kyautata zaton yin hadin kai da wannan cibiya zai taimaka da yaki da ta’addanci a Najeriya.

Gwamnonin Arewacin Najeriya bayan kammala taron da Cibiyar Bunkasa Zaman Lafiya ta shirya
Gwamnonin Arewacin Najeriya bayan kammala taron da Cibiyar Bunkasa Zaman Lafiya ta shirya

Cibiyar, wadda ta shahara wurin tallafawa shirye-shiryen zaman lafiya a duniya, ta ba gwamnonin damar bayyana irin kalubalolin da suke fuskanta domin neman hanyoyin magance matsalolin tsaro a yankin.

A saurari rahoton Baba Makeri:

Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Taimakon Amurka Wajen Shawo Kan Matsalar Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG