Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga-zangar Neman Mayar Da Ndume Majalisa


Zanga zangar kin amincewa da dakatar da Sanata Ndume da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi.
Zanga zangar kin amincewa da dakatar da Sanata Ndume da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi.

Rahotanni daga babban birnin Najeriya Abuja na cewa an gudanar da zanga zangar kira ga Majalisar Dattawan kasar da su janye umurnin dakatar da Sanata Ali Ndume da majalisar ta yi a makon da ya gabata.

Yawancin masu zanga zangar sun fito ne daga yankin kudancin Borno da 'yan gudun hijira dake zaune a Abuja.

An gansu kuma dauke da kwalaye dake nuna kin jinin shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye.

Dubundubatan nutane da suka yi dafifi a kofar Majalisar saboda dakatar da Sanata Ndume da Majalisar tayi
Dubundubatan nutane da suka yi dafifi a kofar Majalisar saboda dakatar da Sanata Ndume da Majalisar tayi

Wani daga kudancin Borno wanda ya fito daga karamar hukumar Gwoza ya ce su ne suka zabe shi suka tura shi Majalisar, saboda haka su ne ya kamata su janye shi.

Masu zanga zangar sun kuma sun gamsu da wakilicin da yake masu.

A makon da ya gabata Majalisar ta dakatar da Sanata Ndume bisa abin da suka kira cewa ya kunyata majalisar a idon duniya yayin wani jawabi da ya yi.

Wata daga cikin masu zanga zangar mai suna Liatu Ayuba, ta yi kira ga Majalisar cikin da ta mayar masu da wakilinsu cikin gaggawa.

To sai dai Majlisar ta tura Sanata Binta Mashi Garba wurin masu zanga zangar da albishirin cewa za ta duba batun dakatar da Sanata Ndume domin a cimma matsaya.

Sanya bakin gwamnan Borno Kashim Shettima da wasu dattawa suka yi ya yi tasiri wajen sassauta matsayin Majalisar wadda a baya ta dauki matakin ba sani ba sabo.

Gabanin wannan zanga zanga, a wata hira ta musamman da yi ya da Muryar Amurka, Sanata Ndume, ya ce shi ba ga laifin da ya yi ba.

"A bisa sani na ni ban yi wani laifi ba." In ji Sanata Ndume, ya na mai cewa bai yi da na sani ba maganar da ya yi wacce masu lura da al'amura suka ce ita ta harzuka 'yan Majalisar.

Domin jin karin bayani saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG